Ban ki-Moon yana ziyara a Burundi

Hakkin mallakar hoto Reuters

Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-Moon,yana wata ziyara a Burundi domin kokarin shawo kan rikicin siyasa a kasar.

Daruruwan mutane sun rasa rayukansu kuma sama da mutane dubu 250 ne suka gudu daga kasar saboda rikicin da ya barke.

Tashin hankalin ya biyo bayan shawarar da shugaba Pierre Nkurunziza ya yanke a watan Afrilun shekarar da ta gabata na tsayawa takara a karo na uku.

Mista Ban zai tattauna da shugabannin jam'iyyu na kasar da kuma kungiyoyin farar hula kafin ya gana da shugaba Nkurunziza a ranar Talata.