IS ta saki wasu Kiristoci a Iraki

Image caption Kiristocin Iraki

Kungiyar IS ta saki wasu kiristoci fiye da 40 da suka yi garkuwa da su kusan shekara daya da ta gabata a Iraki.

Wasu mabiya addinin kirista sun ce sai da aka biya miliyoyin daloli a matsayin diyya domin a saki mutanen, wadanda suka hada da yara da mata.

Suna daga cikinkusan mutane 220 da kungiyar IS ta sace a garin Tel Tamr a arewacin Iraki.

An saki irin wadannan mutane da dama cikin shekara daya da ta gabata, kuma ana ganin wadannan su ne mutane na karshe da suke tsare a hannun kungiyar ta IS.