Modu Sheriff ya karbi ragamar PDP

Image caption Ali Modu Sheriff a yayin da ake rantsar da shi a matsayin sabon shugaban jam'iyyar PDP

A ranar Litinin ne tsohon gwamnan jihar Borno Senata Ali Modu Sharif ya karbi ragwamar shugabancin babbar jam'iyyar adawa a Najeriya ta PDP a hukumance.

Sheriff, wanda ya koma jam'iyyar daga jam'iyyar APC ya karbi ragamar shugabancinta ne daga Prince Uche Secondus, a wajen wani takaitaccen biki a hedikwatar jam'iyyar da ke Abuja.

SAS, kamar yadda ake yi masa lakabi, ya karbi shugabancin jam'iyyar ne bayan da majalisar zartarwar jam'iyyar ta zabe shi a zaman shugabanta a ranar Talatar makon da ya gabata.

Sai dau wasu manyan shugabannin jam'iyyar sun nuna matukar adawa da zaben nasa.

A ranar Lahadi ma wata kungiyar wasu kusoshin jam'iyyar da ake kira PDP Rescue Group, ta yi kira ga Ali Sharif da ya yi murabus.

A cikin jawabinsa ya yi alkawarin sake mayar da jam'iyyar kan turba da kuma mayar da ita jam'iyyar da talakawa za su dinga jujjuya al'amurranta.