"Ba mu yi watsi da batun kamfanin jiragen Nigeria ba"

Image caption Tsohon kamfanin jiragen sama na Nigerian Airways

Hukumar kula da filayen jiragen sama ta Najeriya (FAAN), ta ce gwamnatin tarayya ba ta yi watsi da shirin samar da kamfanin jiragen sama mallakar Najeriya ba.

Hukumar ta ce gwamnatin tarayya tana taka tsantsan a kan lamarin wanda tuni kwamitin da aka kafa ya fara tantancewa da kuma bayar da shawarwarin da za su zama alheri ga kasar.

Hakan dai na zuwa a yayin da 'yan Najeriya ke korafin cewa gwamnati ta yi watsi ko shiru a kan wannan lamari.

Tun bayan da kamfanin jirage Nigerian Airways mallakin gwamnatin kasar ya ruguje dai, ba a kara wani kokari don farfado da shi ba.