Shafukan sada zumunta sun taimaka wa marubuta

Masana da masu mu'amala da shafukan zumunta na zamani sun yi ittifakin cewa shafukan sun taimaka wa marubuta wajen bunkasa ayyukansu.

Sun bayyana haka ne a wajen taro kan shafukan zumunta da ake yi a birnin Lagos da ke kudancin Najeriya.

Daya daga cikin su, Ayo Sogunro, ya shaida wa BBC cewa, shafukan zumunta sun sanya marubuta daga yankunan kasar daban-daban sun kulla dangantaka yadda za su rika musayar bayanai da ra'ayoyi kan rubuce-rubuce.

Sai dai wasu mahalarta taron sun bukaci a daure duk mutumin da ya saci fasahar marubuta daga shafukan zumunta, suna masu cewa hakan zai taimaka wa marubutan wajen kare hakkikinsu. Kazalika, sun yi kira ga masu ruwa-da-tsaki a harkokin yin doka su samar da dokokin da za su kare marubuta na shafukan intanet.