Jirgin ruwan Scotland da ke kai abinci Malawi

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Jirgin ruwan MV Ilala da ke dakon abinci zuwa Malawi

Miliyoyin mutane ne suke fuskantar matsalar karancin abinci a yankin kudancin Afrika a wannan shekarar, sakamakon farin da ya jawo lalacewar amfanin gona.

Wuraren da wannan fari ya fi matukar shafa sun hada da kasar Malawi, wadda ita ce kasar da ta fi kowacce talauci a duniya.

A baya-bayan nan ne Beth McLeod ya yi tafiya har zuwa tafkin Malawi ta wani jirgin ruwan da aka kera a kasar Scotland a lokacin da kasar ke karkashin mulkin Biritaniya.

Ya ce, "Tafiyata ta fara ne daga wani gari Monkey Bay, wanda za a iya cewa sunansa ya dace saboda akwai wasu tarin birrai da ke kai kawo suna kallon kwandunan tumatur din da wasu daga cikin fasinjoji ke dauke da su suna hadiyar yawu.

Wannan ce makura ta kudanci a tafiyata zuwa tafki na uku ma fi girma a Afrika.

Garin da za mu je tafiyar kilomita 480 daga arewaci, kusa da kan iyakar Malawi da Tanzaniya, wanda nake fatan isa cikin kwanaki biyu da rabi.

An gargadeni cewa tafiyar na iya wuce kwanaki biyu saboda jirgin ruwan MV Ilala bai cika bin ka'idar lokacin tafiyarsa ba."

"Jirgin da ya dade yana safara"
Hakkin mallakar hoto Getty

MV Ilala ne jirgin da ya dade yana safara a malawi kuma wanda ya fi kowanne.

An kera jirgin ne a shekarar 1949. Kuma yana da girman da yake iya kwasar fasinjoji da dama.

Bayan fasinjoji, jirgin ya kan kuma dauki kayan abinci da dabbobi wadanda yawnci na fasinjojin ne da za su kai wasu garuruwan domin sayarwa.

Beth McLeod ya ci gaba da cewa, "Mun tsaya ya kai sau goma, wani sa'in a kauyuka ko tsaunuka inda yawanci nan ne mahadar kasar da sauran kasashen duniya."

Akwai wani babban gari a kan hanyarmu wanda yake a da wata gadar da jirgin ke bi a tsakiyar tafkin, amma kwana guda kafin mu karasa garin sai ya afka cikin tafkin.

Hakan ya sa sai da masu kwadago suka shafe dare suna loda masara cikin jirgin ta hanyar amfani da rigar kariya daga nutsewa a ruwa.

An taho da masarar ne daga Zambiya saboda yadda ake karancinta a Malawi.

"Yunwa ta addabi Malawi"
Hakkin mallakar hoto Getty

Hukumar abinci ta Duniya ta yi gargadi cewa kashi 17 cikin 100 na fama da yunwa sakamakon rashin isasshen ruwan sama da aka samu.

Da yawan 'yan Malawi suna shuka masararsu ne domin ciyar da iyalansu., har ma da wadanda suke da wasu ayyukan daban.

Kamar dai yadda wani mutum dan shekar 50 mai suna Gilbert, wanda yake sayar da abinci a cikin jirgin ruwan, ya shaida min cewa, dukkan masarar da ya shuka a garin Monkey Bay bana bai girbi abin kirki ba.

Ya ce min mutane na fama da matsananciyar yunwa, kuma ko a tafki ma ba a cika samu kifi sosai ba saboda masunta sun yi yawa.

Amma wannan masara da aka loda cikin jirgin za a kaita kauyensu Gilbert ne. Kuma ta ruwa ne kawai ake iya kai musu abinci.

Da isar jirgin wata matsayar kuwa yara suka yi cincirindo don sayar da kifi ga fasinjoji.

A lokacin da aka iso matsayata kuwa tuni dare ya yi ni dai na sauka yayin da jirgin ya ci gaba don sauke lodin masarar nan a garuruwan da suke bukata.