An kama jagoran adawa na Uganda

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jagoran adawa Mista Besigye na dagawa magoya bayansa hannu lokacin kamfe

'Yan sanda sun kama babban jagoran 'yan adawa na Uganda, Kizza Besigye.

An kama shi ne a yayin da yake kokarin barin gidansa inda yake fuskantar daurin talala tun ranar Juma'a.

Shugaban Uganda Yoweri Museveni, wanda ya lashe zaben kasar a karo na biyar a makon da ya gabata, ya goyi bayan tsare manyan abokan adawarsa tun bayan da aka kammala zaben.

A wata hira da ya yi da BBC, Mista Museveni ya ce Mista Besigye da kuma tsohon Firai minista Amama Mbabazi, suna aiki tare domin su kunna wutar rikici a kasar.

Sai dai masu sa ido a zaben daga kasashen duniya sun ce zaben yana cike da magudi.