Binciken wayar wanda ya yi kisa

Bill Gates Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Bill Gates

Shahararren attajirin nan mai Kamfanin Microsoft, Bill Gates ya ce kamata ya yi cece kucen da ake yi tsakanin kamfanin Apple da Hukumar bincike ta FBI ya janyo muhawara kan bukatar mahukunta na samun damar binciken wayar wanda ya yi kisa.

Hukumar FBI na bukatar kamfanin Apple ya bude mukullin sirri a wayar iPhone ta Syed Rizwan Farook wanda ake zargi da kashe mutane goma sha hudu a watan disamban bara.

Kamfanin Apple dai ya ki amince wa da bukatar yana mai cewa umurnin da hukumar bincike ta FBI ta bada na da matukar hadari.

Da yake magana da mujallar Financial Times, Bill Gates ya ce bukatar neman binciken wayar ba ta da bambamci da bukatar da kamfanonin wayar salula da bankuna ke yi na samun bayanai.