Nakasassu sun yabawa Buhari

Image caption Shugaba Buhari ya bai wa daya daga cikin nakasassu mukamin mataimaki na musamman

Masu bukatu na musamman a Najeriya sun bayyana jin dadinsu da mukamin mataimaki na musamman da Shugaba Muhammadu Buhari ya bai wa daya daga cikinsu.

A farkon makon nan ne dai Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Dr Samuel Inalegwu Ode Ankeli, wanda makaho ne, a matsayin babban mataimaki na musamman a kan al'amuran da suka shafi nakasassu.

Wannan ne dai karo na farko da aka taba bai wa wani mai nakasa mukami irin wannan a Najeriya.

Isyaku Adamu Gombe shi ne shugaban Kungiyar Makafi ta Kasa, kuma ya yi wa Yusuf Tijjani karin bayani ta wayar tarho kan yadda suka ji da wannan nadi.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti