Za'a sanya dokar yin wa'azi a Kaduna

Malam Nasir El Rufai Hakkin mallakar hoto kaduna govt
Image caption Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El Rufai

Gwamnatin jahar Kaduna ta gabatar da wani kudirin doka ga majalisar dokokin jahar da nufin sa ido kan yadda malamai na addini Musulunci da kiristoci ke wa'azi.

Gwamnatin jihar ta ce ta dauki wannan mataki ne sakamakon koke koke kan yadda wasu malaman addinan biyu ke amfani da amsa kuwwa a masalatai da majami'u da kuma wa'azi mai tada hankulan jama'a ba tare da samun lasisi ba.

Kudirin in ya zama doka ya tanadi dauri ko tara ga wanda aka samu da keta dokar.

Anata bangaren Majalisar Malamai da Limamai ta jihar Kaduna ta ce tana nazari game da tanadin dokar kuma nan gaba kadan za ta bayyana matsayin ta game da dokar.