Ana zargin dagaci da lalata da yarinya a Kano

Image caption Sarkin Kano Muhammadu Sunusi

Majalisar masarautar Kano ta dakatar da wani dagaci bisa zarginsa da yin lalata da wata yarinya 'yar shekara 13 tare da sa mata cutar HIV.

Galadiman Kano kuma babban dan majalisar Sarki Alhaji Abbas Sanusi, shi ne ya dakatar da dagacin.

Korafi a hukumar Hizbah.

Darakta Janar na hukumar ta Hizbah Malam Abba Kabiru Sufi, ya shaida wa BBC cewa iyayen yarinyar ne suka kai musu korafi, inda suka ce a asibiti an tabbatar musu da cewa yarinyar na dauke da cutar ta Sida.

Daga nan ne kuma aka mika dagacin zuwa fadar masarautar Kano.

Babban kwamandan hukumar Hizba Shaikh Aminu Ibrahim Daurawa ya yiwa wakilin mu Yusuf Ibrahim Yakasai karin bayani kan yadda lamarin ya faru.
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti