Ministocin PDP ba su yarda da Sheriff ba

Image caption Tsoffin ministocin PDP ba su amince da zaben Ali Madu Shariff ba

A Najeriya, wasu 'ya'yan babbar jam'iyyar adawa a kasar wato PDP na ci gaba da nuna rashin amincewar su da nadin da aka yi wa Senata Ali Modu Sharif a matsayin shugaban jam'iyyar.

Hakan ya kara fitowa fili ne bayan da Kungiyar tsoffin ministocin gwamnatocin jam'iyyar a wani taro a Abuja, mambobin kungiyar suka nuna rashin amincewar su da nadinsa a zaman shugaban jam'iyyar, inda suka ce an karya ka'idojin kundin tsarin mulkin jam'iyyar wajen zabarsa a matsayin shugaba.

Alhaji Kabiru Tanimu Turaki, tsohon ministan ayyukka na musamman, shi ne shugaban kungiyar, ga kuma karin bayanin da ya yi wa Haruna Shehu Tangaza;

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti