Za a tsagaita wuta na dan lokaci a Syria

Hakkin mallakar hoto AFP GETTY
Image caption An shafe kusan shekaru biyar ana yakin basasar da ya ki ci ya ki cinyewa a Syria

Gwamnatin Syria da babbar kungiyar adawa ta HNC da kuma kungiyar 'yan tawaye ba su nuna cikakkiyar amincewarsu kan yarjejeniyar tsagaita wutar da amurka da Rasha suka sanar ba.

Amma gwamnatin ta ce dakatar da ayyukan nata bai hada da kai hari kan kungiyoyin IS da ta Al-Nusra mai alaka da Al-Qaeda ba.

Kungiyar 'yan adawar HNC, ta ce ta amince da yarjejeniyar tsagaita wutar ta dan lokaci ya ne kan sharadin gwamnatin Syria za ta kawo karshen kawanyar da ta yi wa yankuna 18 da ke karkashin ikon 'yan tawaye.

Haka kuma gwamnatin za ta saki fursunoni da kuma dakatar da kai hare-hare ta sama da ta kasa.

Tun a baya dai ake ta son cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin gwamnatin Syria da 'yan tawaye amma sai a tashi baram-baram.