Al'ummar Bolivia sun yi watsi da tazarcen Morales

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Evo Morales na son tazarce

Masu kada kuri'a a Bolivia sun yi watsi da batun canja kundin tsarin mulkin kasar da zai ba wa shugaba Evo Morales damar tsayawa takara a karo na hudu.

Kusan dukkan kuri'un jin ra'ayin jama'ar da aka kirga da adadinsu ya kai kaso 51.3 cikin 100 sun yi watsi da batun.

Amma Morales na bukatar sake tsayawa takarar shugabancin kasar tun bayan zaben sa na farko a shekarar 2006.

Mr Morales wanda shi ne shugaban kasar ta Bolivia na farko da ya kasance dan asalin kasar ya ce zai girmama sakamakon kuri'ar jin ra'ayin jama'ar da aka gudanar.

Idan aka canja kundin tsarin mulkin kasar, zai ba shi damar sake tsayawa takara a zaben shekarar ta 2019, inda zai kasance a mulki har shekarar 2025.

Masu sanya idanu a kan zaben kuri'ar jin ra'ayin jama'ar sun ce kirga kuri'un na tafiyar hawainiya, sai dai kuma ba bu wata alama da ta nuna cewa akwai magudi a ciki.

Masu bincike sun ce akwai yiwuwar wadanda basu amince ba za su iya yin nasara bisa la'akari da iya adadin kuri'un aka kirga kawo yanzu.