Compaore ya zama dan Ivory Coast

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Blaise Compaore ya zama dan Ivory Coast

Al'ummar Burkina Faso sun sha mamaki kwarai kuma ra'ayoyinsu sun bambanta kan labarin cewa hambararren shugaban kasar Blaise Compaore, ya zama dan Ivory Coast.

Compaore ya samu takardar shaidar zama dan Ivory Coast ne makonni biyu bayan ya bar kasarsa sakamakon tashin hankalin da ya faru a watan Oktobar 2014.

A watan Disambar bara ne jami'ai a Burkina Faso suka bayar da sanarwar neman kama Mista Compaore saboda bijirewar da ya nuna kan rikicin da ya kai ga hambarar da shi.

Wani mamba na kungiyar fararen hula Ismael Diallo, ya ce, "Yana da damar yin hakan amma me yasa ya yi? Ba dai wai don ya zama dan Ivory Coast ba sai dai saboda yana son gujewa tsarin dokar kasarsa."

Kungiyoyin fararen hular dai na ganin wannan hukunci da Mista Compaore ya dauka abin kunya ne.