'Za a hukunta wadanda suka sauya kasafin Nigeria'

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugaba Buhari a lokacin da yake gabatar da kasafin kudin ga shugaban majalisar dattawa

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya sha alawashin daukar tsattsauran matakin ladabtarwa kan duk masu hannu a sassauya alkaluman kasafin kudin kasar na shekarar 2016.

Muhammadu Buhari ya yi wannan furuci ne a lokacin da ya gana da 'yan Najeriya mazauna kasar Saudiyya ranar Talata, inda ya yi Allah-wadai da sauye-sauyen da aka yi wa kasafin kudin.

Shugaban ya kara da cewa sauye-sauyen da aka yi ta bayan fage su ne suka sa kasafin kudin ya bambanta da wanda ya gabatar wa majalisar dokokin kasar.

''Wadanda suka tafka wannan danyen aikin ba za su sha ba, sai an hukuntasu. Na yi gwamna na mulkin soji, na kuma rike mukamin ministan albarkatun mai da ma na shugaban kasa a karkashin mulkin soji, sannan kuma na shugabanci asusun rarar kudin man Fetur; amma ban taba jin wannan kalmar ta Budget Padding ba,'' In ji shi.

Shugaba Muhammadu Buhari ya kuma jaddada anniyarsa ta yaki da cin hanci da rashawa a kasar.