Kyautar tunawa da Komla Dumor ta 2016

Hakkin mallakar hoto
Image caption Gwarzo Komla Dumor

Kyautar tunawa da Komla Dumor: BBC na neman gwarzon dan jarida na Afrika na shekarar 2016, wanda za a bayar a karo na biyu a wannan shekarar.

BBC tana neman gwarzon dan jarida na Afrika da za a bai wa kyautar tunawa da Komla Dumor karo na biyu.

Duk wanda ya lashe kyautar zai yi aiki da ma'aikatan sashen labarai a BBC London na tsawon watanni uku.

Wadda ta lashe kyautar a bara Nancy Kacungira, ta ce, "Na samu goyon baya matuka a matsayina na 'yar jarida daga nahiyar Afrika, inda na yi labarin da nake so na fada ta hanyar da nake ganin ya dace a fadi labarin."

Za a rufe shiga gasar ranar 23 ga watan Maris 2016 da misalin karfe 11.59 na dare agogon GMT, wanda ya yi daidai da 12.59 na dare agogon Najeriya.

An fito da gasar ne domin girmama Komla Dumor, mai gabatar da shirye-shirye a BBC, wanda ya yi mutuwar bagatatan a shekarar 2014, yana dan shekara 41.

Image caption Nancy Kucungira ce ta lashe kyautar Komla Dumor ta bara

An zabi Ms Kacungira mai gabatar da shirye-shirye a gidan talabijin na kasar Kenya daga cikin mutane kusan 200 da suka shiga gasar.

Ta ce, "Abin jin dadi kwarai a ce ka samu damar bayar da labari daga Afrika a irin wannan babban waje - an nuna kuma an yada labarin da na yi a tasoshin talabijin na bBC da rediyo da kuma intanet."

Ta kara da cewa, "Nawa ma'aunin na rahotanni a kan nahiyar Afrika inda nakan tantance rahotanni don sahihanci da kuma ji daga dukkan bangarori, ya dace da tsarin BBC na tabbatar da gaskiyar rahoto daga duk inda suke samo labarai."

Shugabar Sashen BBC mai watsa labarai ga kasashen duniya, Fran Unsworth, ta ce "Komla dan jarida ne abin tunawa da girmamawa, ba wai a wajen abokan aikinsa ba kawai, har ma a wajen sauran 'yan jarida da masu saurare da ke son ci gaba a ko ina cikin duniya.

Ta kara da cewa, "Labaransa na cike da hikima da kayatarwa, wanda hakan ya sa ya zama daya daga cikin manyan 'yan jarida a Afrika."

Image caption Shugabar Sashen BBC mai watsa labarai ga kasashen duniya, Fran Unsworth kenan

Misis Unsworth ta ce, "Mu a BBC muna kokari domin ganin mun ci gaba da sadaukar da kokarin Komla ga Afrika ta hanyar kaddsamar da wannan lambar yabo a karo na biyu. Muna neman dan jarida ko 'yar jarida hazikai, wadanda suke da irin kwazon Komla."

Komla Dumor dai dan jaridar kasar Ghana ne wanda ya yi aiki tukuru da kwazo a iya rayuwarsa, ya kuma fito da kasarsa da nahiyar Afrika a duniya ta hanyar labaransa.

A baki dayan rayuwarsa ta aikin jarida, Komla ya yi aiki ba gajiyawa domin fito da labaran ci gaban Afrika.

BBC za ta ci gaba da tunawa da abubuwan tarihi da Komla ya bari.

Duk masu son shiga gasar da suka cika sharuda suna da lokaci har nan da karfe 12.59 na dare agogon Najeriya, ranar 23 ga watan Maris 2016.