Jama'ar Nigeria sun koka kan cire kudi a wayoyinsu

A Najeriya, 'yan kasar na kokawa dangane da yadda kamfanonin wayar sadarwa ke cire wa jama'a kudi a layukan wayoyinsu.

Jama'a sun koka kan samun sakonni da suka kira marasa kangado, da sanya sauti ba tare da sun bukaci hakan ba ko tura musu tallace-tallace, ko kuma cire kudi duk da cewa ba sa jin maganr wanda suka kira.

A wani mataki na nuna fushinsu ne a kan wannan lamari wasu 'yan kasar suka fito da wani maudu'i a dandalin sa da zumunta da muhawara na Twitter.

Sai dai hukumar sa ido kan kamfanonin a kasar, NCC ta ce tana shirin maganin wannan matsalar.

Ga dai ra'ayoyin wasu 'yan Najeriya game da wannan batu.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti