Xiaomi ya fitar da wayar Mi5

Hakkin mallakar hoto miindiaFB
Image caption Xiaomi ya ce shine na 5 cikin jerin fitattun kamfanonin da aka fi sayen wayar salular su a duniya

Kamfanin Xiaomi na kasar China ya fito da wayar salula samfurin Mi5 da aka yi da tangaran.

Kamfanin ya fitar samfurin wayar ta Mi5 ne a wani taron manema labaru don kaddamar da wayar salular a Beijing da kuma taron koli kan wayoyin salula a Barcelona.

Xiaomi ya bayyana kansa a matsayin kamfani da ke mataki na biyar cikin jerin fitattun kamfanonin da aka fi sayen wayar salular su a duniya.

Kamfanin IDC mai bincike akan kasuwannin ya ce wayoyin salular da kamfanin Xiaomi ya fitar a bara ya kai kashi 23, wanda ya nuna cewa kamfanin ya sayar da kashi 5 cikin 100 na wayoyin salular da aka sayar a kasuwannin duniya.