Shugaban kamfanin Apple ya kare matakin kin amincewa da bukatar FBI

Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaban kamfanin Apple ya ki amincewa da bukatar FBI

Shugaban kamfanin Apple ya sake kare matakin da kamfanin ya dauka na kin amincewa ya taimaka wa hukumar bincike ta FBI bude wayar wasu ma'aurata da suka hallaka mutane goma sha hudu a California bara.

Hukumar FBI tana bukatar kamfanin Apple ya bude mukullin sirri a wayar iPhone ta Syed Rizwan Farook wanda ake zargi da kashe mutane goma sha hudu a watan Disambar bara.

Sai dai a hira da ya yi da kafar yada labarai ta ABC News, Tim Cook ya ce yin hakan zai jefa masu amfani da wayar salular a Amurka dama sauran kasashen duniya cikin hadari.

Ya ce wannan matsala ba wai kawai ta tsaya ne ga wayar mutum guda ba, ta shafi abubuwan da zasu iya faruwa ne anan gaba.