India: Yara sun ci gurbataccen abinci

Hakkin mallakar hoto AP

'Yan sandan jihar Maharashtra da ke kasar Indiya sun ce an kwantar da yara kusan 100 a asibiti.

Ana zargin yaran sun ci gurbatacen abincin rana ne a makarantar gwamnati.

Rahotanni sun ce wasu daga cikinsu na cikin mummunan yanayi.

Za a yi gwaji a kan kadan daga cikin abincin da yaran suka ci.

A shekaru uku da suka wuce, ne dai sama da yaran makarantar da ke lardin Bihar 20, suka rasa rayukansu bayan sun ci abinci mai maganin kwari.

Karin bayani