Ana saba dokokin hanya a jihar Kano

Image caption 'Yan Karota a jihar Kano

Jihar Kano a arewacin Nigeria ita ce jihar da tafi sauran jihohin kasar yawan jama'a, inda mafi yawan jama'ar ke zaune a babban birnin jihar.

Hakan dai ya haifar da karuwar ababen sufuri a birnin.

Alkaluma sun nuna cewa ana samun karuwar saba dokokin hanya, duk kuwa da hukumomin jihar sun kafa hukumomin dake kula da tuki.

Barista Lamido Abba Soron Dinki, shi ne sakataren hukumar da ke kula da sufuri da aka fi sani da Karota, sannan kuma shi ne mai bada shawara ta fuskar shari'a , ya yiwa Yusuf Ibrahim Yakasai karin bayani a kan irin laifukan da aka fi yawan aikatawa a kan titunan jihar ta Kano, ga kuma yadda tattaunawar ta su ta kasance;

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti