Kenyatta ya zargi 'yan kasarsa da mugun hali

Hakkin mallakar hoto PSCU Kenya
Image caption Kenyatta ya ce 'yan kasarsa sun kware a cin hanci

Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta, ya zargi 'yan kasarsa da cin hanci da rashawa da kuma aikata sauran miyagun laifuka.

Da yake yi wa 'yan Kenya mazauna Isra'ila jawabi a wata ziyara da ya kai, Mista Kenyatta ya ce 'yan kasarsa basu da wani aiki a duk inda suke da ya wuce sata da korafi.

Ya ce, "'Yan Kenya kwararrun barayi ne da cin zarafi, kuma masu son nuna kabilanci, sannan kuma kasar ta fi ban sha'awa sau 20 a lokacin samun 'yancinta fiye da yanzu."

A bara ne shugaba Kenyatta ya kori wasu ministocinsa da jami'an gwamnati kan zargin cin hanci da rashawa.

Karin bayani