An kammala taro a kan allurar rigakafi

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An kammala taro domin inganta allurar rigafi a Afrika

Ministocin lafiya da sauran masu ruwa da tsaki a harkar kiwon lafiya a nahiyar Afirka sun kammala wani babban taro a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, inda suka tattauna a kan dukkan batutuwan da suka shafi alluran riga-kafi.

Za a dai a iya kaucewa kamuwa da cututtuka irin su sankarau, da shan-inna, wato polio, da kuma ciwon hanta ta hanyar yin wadannan alluran riga-kafin, kuma kasashen Afirka sun yi nasara a bangarorin riga-kafin da dama a 'yan shekarun nan.

Sai dai har yanzu an yi kiyasin cewa yaro daya a cikin duk yara biyar a nahiyar ba sa samun alluran riga-kafin da suke bukata.

Amma a Najeriya kashi daya a cikin uku na yara ne ba sa samun riga-kafin.

Ministan lafiya na Najeriya, Farfesa Issac Adewole ya halarci taron, kuma ya yi karin bayani a kan dalilin da ya sa Najeriya ta zama kurar baya a tsakanin galibin kasashen Afrika a bangaren allurar rigafin cututtuka, ga kuma abinda ya ke cewa;

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Karin bayani