An kusa bayyana sakamakon Niger

Hakkin mallakar hoto Getty

Hukumar zaben Jamhuriyar Nijar, CENI, ta sanar da kashi 70 cikin 100 na sakamakon zaben shugaban kasar da aka yi a ranar Lahadi.

Hukumar ta ce sakamakon da ke hannunta ya nuna cewa Shugaba Muhamadou Issoufou na jam'iyyar PNDS, ya samu kashi 46.16

A cewar ta, Malam Hama Amadou na jam'iyyar Moden Lumana party, wanda ke tsaro a kurkuku, ya samu kashi 16.53, yayin da Seyni Oumarou na jam'iyyar MNSD ya zo na uku, inda ya samu kashi 11.44.

Shugaban hukumar zaben, Bube Ibrahim, ya shaida wa BBC cewa ana sa ran sanar da duk kan sakamakon zaben ranar Alhamis.

An dauke Hama Amadou ne ana zargin sa da hannu a safarar jarirai daga Najeriya, ko da ya ke ya musanta zargin, yana mai cewa bita-da-kullin siyasa ne kawai.

Karin bayani