Zaben Niger: Ko za a je zagaye na biyu?

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Hama Amadou na tsare a gidan kaso aka yi zaben

An bayyana kashi 70 cikin dari na sakamakon zabe a Nijar, amma kawo yanzu cikin manyan 'yan takarar biyu da kuma shugaban kasar mai ci babu wanda ya samu kaso 50 cikin dari da ake bukata.

Idan hakan bai samu ba to dan takarar da yafi samun kuri'u da wanda ke biye masa za su je zagaye na biyu a ranar 20 ga watan Maris.

Sakamakon da hukumar zabe ta kasar CENI ta fitar ya nuna cewa shugaba Mahamadou Issoufou na jam'iyyar PNDS Tarayya ya samu kashi 46.16 na kuri'un da aka kada a ranar Lahadi.

Yayin da shi kuma Hama Amadou na jam'iyyar Moden Lumana ke biye masa da kashi 16.53 cikin dari.

Sai Seyni Oumarou na MNSD Nasara wanda ke matsayi na uku da kashi 11. 44 cikin dari.

Tuni dai jinkirin da ake samu wajen tattara sakamakon zaben ya janyo cece-kuce a kasar.