Bam ya kashe 'yan sanda a Jimeta

Hakkin mallakar hoto Getty

Rahotanni daga Jimeta a jihar Adamawan Najeriya na cewa wasu jami'an 'yan sanda sun rasa rayukansu sakamakon tashin wani bam a hedikwatar hukumar 'yan sanda da ke garin.

Gwamnatin jihar Adamawa dai ta bayar da tabbacin cewa ba harin ta'adanci ba ne, bam din ya tashi ne a matattarar bama-bamai ta 'yan sanda na Jimeta Division.

Harin ya kuma shafi wata makaranta da ke kusa da ofishin 'yan sandan.

Kwamishinan yada labarai na jihar Adamawa Ahmad Sajo, ya shaida wa BBC cewa, babu yaron makaranta da ya rasu a lokacin da bam din ya fashe, wasu kalilan ne suka ji rauni, kuma ana yi musu magani.

Kwamishinan ya kuma ce za su gana da hukumomin 'yan sanda nan gaba don daukar matakan kaucewa sake faruwar hakan nan gaba.

Wasu mazauna yankin sun shaida wa BBC cewa jami'an yan sanda sun killace yankin a yanzu.