'Yan sanda hudu sun mutu a harin Jimeta

Image caption Bam din ya tashi a matattarar bama-bamai ta ofishin 'yan sanda a Jimeta

Akalla mutane hudu ne suka mutu sakamakon bam din da ya tashi a matattarar bamabamai ta 'yan sanda ta Jimeta Division a jihar Adamawa a safiyar yau.

A hirar da ya yi da Halima Umar Saleh, kwamishinan yada labarai na jihar Alhaji Ahmed Sajoh, ya shaida mata cewa wadanda suka jikkata kuma a yanzu haka suna karbar magani a babban asibitin gwamnatin tarayya da ke Yola.

Ga dai yadda hirar tasu ta kasance:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti