Apple ya nemi kotu ta janye umurnin FBI

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Apple ya ce hukumomin tsaro na neman a ba su iko mai hadari wanda ya saba doka.

Kamfanin Apple ya bukaci wata kotu a Amurka da ta soke umurnin da ta ba kamfanin na ya taimaka wa hukumar FBI don bude wayar wani da ake zargi da hallaka mutane goma sha hudu a California bara.

Apple ya ce hukumomin tsaro na neman a ba su iko mai hadari kuma yin hakan ya saba wa doka.

Hukumar FBI da kuma fadar White House sun ce bukatar bude wayar ta shafi wayar iPhone ta mutum guda ne kawai.

Sai dai kamfanin Apple ya ce babu wa ta kotu da ta taba tilasta wa kamfanin rage matakan kariya akan kayayyakin da kamfanin ke sayar wa don samun damar binciken bayanan wani da ke amfani da wayar kamfanin.