An soki EDF da nuna son kai a gasa tsakanin yara Maza da Mata

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kamfanin EDF

Ana sukar kamfanin makamashi na EDF bayan ya ayyana yaro dan kimanin shekaru goma sha uku da haihuwa a matsayin wanda ya lashe wata gasa wadda bangare ce ta jan hankalin yammata su shiga fagen kimiyya da fasaha dama darasin lissafi a dama da su.

An dai bukaci yaran da su je suyi tunani a kan kirkiro da kayayyakin da ake ajiwa a dakunan kwana wadanda ba bu irinsu.

Kamfanin EDF ya ce tunda shirin an kirkiro shi ne da nufin jan hankalin yara mata, to har yanzu yana kan bakar sa, kuma kofa a bude take ga duk wadda zata shiga gasar in dai shekarunta ba su wuce 11 zuwa 16 ba.

Sakamakon nasarar da aka samu a gasar da aka shirya har sau uku a Birtniya inda yammata suka fafata a shekarar data wuce, yanzu an fadada shirin kuma yara maza ma za su iya shiga gasar.

Yammata hudu daga cikin wadanda suka fafata a gasar, sun bayar da ra'ayoyinsu akan yadda za a samar da labulaye na alfarma da Fiijin alfarma da kuma na'urar da ke kula da mutum idan yana barci.