An daura auren Ishaq Sidi Ishaq

Hakkin mallakar hoto Ishaq Sidi Ishaq
Image caption Ango Ishaq 'Dan Kwalisa' da abokansa bayan daura auren, a Minna ta Jihar Niger, Najeriya

An daura auren fitaccen darakta kuma dan wasan Hausa, Ishaq Sidi Ishaq, wanda aka fi sani 'Dan kwalisa' ko ISI.

A ranar Juma'a ne aka daura auren 'Dan kwalisa' da kuma Nasiba Usman Wada.

An daura auren ne a Unguwar Daji da ke birnin Minna na jihar Naija bayan sallar Juma'a.

A hirarsa da BBC, Ishaq ya ce, amarya Nasiba 'yar alkali Usman Wada ce, Salanken Minna, ba kuma 'yar fim ba ce kamar yadda mutane ke tsammani.

Ishaq Sidi Ishaq, fitaccen darakta a Kannywood, na daya daga cikin 'yan fim din da suka dade ba su yi aure ba.