Za a je zagaye na biyu a zaben Nijar

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Hukumar zaben Nijar ta ce babu dan takarar da ya samu kashi 50 na kuri'un da aka kada.

Hukumar zaben Jamhuriyar Nijar ta ce za a je zagaye na biyu na zaben shugaban kasar bayan da aka rasa samun dan takarar da ya samu kashi 50 cikin dari na kuri'un da aka kada.

Shugaban kasar Mahamadou Issoufou ya samu kashi 48.4, yayin da Hama Amadou ya samu kashi 19, sai kuma Seyni Oumarou da ya samu kashi 12.

Shugaban hukumar zaben ya ce za a yi zagaye na biyu ne ranar 20 ga watan Maris.