Tsokacin 'yan Nijar kan sakamakon zabe

Image caption Al'ummar Nijar sun banbanta a ra'ayi dangane da sakamakon zaben shugaban kasar da aka gudanar

A Jamhuriyar Nijar an soma mayar da martani ga sakamakon zaben shugaban kasar da aka sanar, wanda ya nuna cewa babu wanda ya samu nasara, abin da ke nuna sai an je ga zagaye na biyu na zaben.

A yammacin ranar Jumma'a ne dai hukumar zaben kasar watau CENI, ta bayyana sakamakon zaben inda shugaban kasar mai ci, Mahammadou Issoufou, ya kasa samun nasara a bugu daya, duk da cewa shi ya fi samun kuri'u.

To dangane da wannan batu na sakamakon zaben Nijar din, wakiliyarmu Tchima Illa Issoufou ta tattaro mana ra'ayoyin 'yan Damagaram, ga kuma abinda wasun su ke cewa;

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti