"Dokar kafofin sada zumunta ba za ta yi nasara ba"

Shugaban majalisar dattawan Nigeria, Sanata Bukola Saraki, ya ce majalisar za ta yi watsi da dokar nan mai son a takaita amfani da shafukan sada zumunta da muhawara.

Sanata Saraki ya bayyana hakan ne a jawabin da ya yi wajen taron makon sada zumunta da muhawara a birnin Lagos.

Ya jaddada cewa ana samun karuwar masu amfani da wadannan shafuka musamman ta fuskar gyaran siyasar Najeriya, kuma tattaunawar da ake yi a kafofin na kawo ci gaba sosai a kasar.

"Sun taka rawa a zaben 2015"

Sanata Saraki ya kara da cewa, "In ba don amfani da kafofin sada zumunta ba, da ba a samu irin sauyin gwamnatin da ake so ba a kasar nan."

Ya kuma jinjinawa masu amfani da shafukan, inda ya kira su 'Shugabannin hukumar zabe,' yana mai cewa, "kokarin da suka yi wajen bayyana sakamakon mazabu daban-daban a kafofin, ya taimaka sosai wajen hana tafka magudi."

Shugaban ya tabbatarwa 'yan Najeriya cewa wannan kudurin doka na takaita amfani da kafofin sadarwa ba zai tsallake ba a majalisar.

Kazalika, ya ce nan da makonni kadan za a cimma bukatar nan ta bankada dukkan abin da ke faruwa a majalisar kasar ga jama'a.

Sanata Saraki shi ne shugaban al'umma na farko da ya taba halartar taron makon kafofin sadarwa na zamani da aka yi karo na hudu a wannan shekarar.

Karin bayani