Amurka na son MDD ta sanyawa Korea takunkumi

Image caption Samantha Power ta ce dole Koriya ta arewa ta dau alhakin laifinta

Amurka tare da goyon bayan kasar China sun mika wani kuduri ga kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya wanda zai sanya takunkumi mai tsauri a kan Koriya ta arewa.

Wannan yunkuri ya biyo bayan kaddamar da gwajin makamin nukiliya da kuma roka da Koriya ta arewan ta yi ne a baya-bayan nan.

A cikin kudurin akwai matakai da suka hada da duba duk wani jirgin dakon kaya da zai shiga ko fita daga cikin Koriya ta arewan, tare kuma da haramta sayar da makamai.

Jakadiyar Amurka a MDD Samantha Power, ta ce tilas a dorawa Koriya ta arewa alhakin matakin da ta dauka.

Ta ce, "Muna fatan kada kuri'a nan gaba kadan. Yanzu makwanni bakwai kenan tun bayan gwajin makamin nukiliya da Koriya ta arewan ta yi, kuma mun yi nazari sosai akan wadanan kwanaki da aka yi gwajin."

Karin bayani