Sojoji za su fara aiki da babura dan yakar BH

Sojojin Najeriya a bakin daga. Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sojojin Najeriya sun kunutar da mutane da dama da aka yi garkuwa da su.

Rundunar sojin kasa ta Najeriya ta kaddamar da sojoji na musamman masu amfani da babura da nufin farautar mayakan boko haram a wasu lunguna da sako da ke arewa-maso-gabashin kasar.

Kazalika rundunar ta fitar da jerin hotunan wasu mutane da take zargin cewa 'yan kungiyar ne da take nema ruwa-a-jallo.

Kakakin rundunar, Kanar Sani Usman Kukasheka ya shaidawa BBC cewa wani sabon salo ne na kakkabe kungiyar Boko Haram.

Musamman yanzu da aka ci galabar 'yan kungiyar, da suke shiga lungu da sako na garuruwa dan yin fashi da makami.

Dan haka wannan babur ya na dauke da makamai masu cin dogon zango a jikinsu, da kuma na'urori da za su taimaka dan gano maboyar masu 'yan ta'addan.

Kukasheka ya yi kira ga al'umar Nigeri su bai wa sojoji da jami'an tsaro hadin kai dan kawo karshen kungiyar Boko Haram, ta hanyar bayar da bayanan da za su taimaka wajen wannan aiki.