AU za ta tura jami'an sa ido Burundi

Hakkin mallakar hoto AFP

Kungiyar tarayyar Afirka ta ce za ta tura jami'ai kimanin 100 masu sa ido kan kare hakkin bil Adama da kuma sojoji 100 domin sa ido a kan yadda al'amura ke gudana a Burundi.

Kungiyar ta ce shirin tura jami'an ya sami goyon bayan shugaban kasar Pierre Nkurunziza.

Shugaban Afirka ta kudu Jacob Zuma ya jagoranci tawagar shugabanni kasashe biyar na Afirka a wata ziyarar kwanaki biyu a kasar a cikin wannan makon.

Sun gana da Mr Nkurunziza da kuma shugabanni biyu na yan adawa wadanda suka zauna a kasar duk da rikicin da ya barke a watan Aprilun bara lokacin da shugaban ya sanar da cewa zai sake tsayawa takara karo na uku.

Sun kara da cewa nan ba da jimawa ba mai shiga tsakani na kungiyar tarayyar Afirka kuma shugaban kasar Uganda Yyoweri Museveni zai shirya wata tattaunawa da za ta kunshi dukkan bangarori.