Ana ci gaba da kidayar kuri'a a Iran

kidayar kuri'u a Iran Hakkin mallakar hoto Iran
Image caption Ana dakon sakamakon zaben Iran.

A kasar Iran, an ci gaba da kidayar kuri'un da aka kada a zabe na farko da aka gudanar a kasar bayan yarjejeniyar da kasar ta cimma da manyan kasashen duniya a kan shirinta na nukiliya.

A zaben majalisar dokoki dai masu ra'ayin sauyi, wato magoya bayan shugaba Hassan Rouhani sun kama hanyar samun gagarumar nasara a Tehran, Babban birnin kasar.

Kazalika an yi zaben kwamitin shugabannin addini, wadanda ke da alhakin nada shugaban addini na kasar.

Kuri'un farko da aka kidaya dai sun nuna cewa shugaban kasar mai ra'ayin sauyi, wato Hassan Rouhani da kuma tsohon shugaban kasar Ayatullah Akbar Hashemi Rafsanjani suna samun nasara a Tehran da kewaye.