Buhari ya nemi OPEC ta canja salo

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya ce dole ne kungiyar kasashe masu hako man fetur (wato OPEC) ta dauki matakin da zai kawo dagawar farashin mai a duniya.

Farashin man ya fadi da kimanin kashi 70 bisa 100, inda yanzu ake saida gangar man dala 35 -- lamarin da ke baraza sosai ga tattalin arzikin Najeriya.

Shugaba Buharin, wanda ke ziyarar kasar Qatar, ya gaya wa Sarkin Qatar, Sheikh Tamim Bin Hammad Al-Thani, dole su dauki matakin da zai daga farashin man.

Ya ce kama ya yi kungiyar OPEC ta hada kai da kasashen nan masu tono mai wadanda basu cikinta domin fuskantar matsalar.

Wata sanarwa daga mai baiwa Shugaba Buharin shawara kan harkokin yada labarai, Femi Adeshina, ta ruwaito shugaban yana cewa ba zai yiyu ba a bar farashin mai ya barbare haka ba.

Ya ce samun hadin kan kasashe masu hako man ne zai taimaka wajen dago da farashin.