Masu ra'ayin sauyi sun yi nasara a zaben Iran

Hassan Rouhani na kasar Iran
Image caption Hassan Rouhani na kasar Iran

Yayinda ake ci gaba da kidaya kuri'u a zaben kasar Iran, ana ci gaba da samun karin haske akan yadda masu tsatsauran ra'ayi suka sha kaye.

Biyu daga cikin manyan malamai masu tsatsauran ra'ayi sun rasa kujerunsu a zaben majalisar da ke da karfin fada- a -ji wajen nada shugaban adini na kasar.

Masu mastaikacin ra'ayi da kuma masu ra'ayin kawo sauyi da ke goyon bayan Shugaba Hassan Rouhani sun samu galaba a zaben Majalisar dokokin kasar.

Alamu na nuni da cewa Mista Rouhani zai samu dan karamin rinjaye, lamarin da zai kasance babban komabaya ga masu ra'ayin rikau.