Za a kafa dokar wa'azi a Kaduna

Malam Nasiru El-Rufa'i Hakkin mallakar hoto Nasir ElRufai Facebook
Image caption Gwamnati ta ce ta na son tankade da rairaya kan mutanen da ke gudanar da harkokin addini a jihar.

Gwamnatin jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya, ta yi bayani a kan dokar nan da ta mika wa majalisar dokokin jihar mai neman sa-ido a kan yadda wasu ke gudanar da harkokin addini a jahar.

Gwamnatin wadda ta ce tana kokarin kafa dokar ne domin gyara zamantakewar al'umma, ta ce yanzu wasu na neman amfani da wannan batu domin cimma wani buri na siyasa.

Batun wa'azi da batanci, da amfani da amsa kuwwa a Coci-coci da masallatai ba tare da la'akari da hakkkokin wasu jama'a ba, na cikin abubuwan da gwamnatin ta ce tana kokarin daukan mataki a kai, sai dai wasu a jahar na cewa tsarin mulkin kasa ya ba wa kowa damar yin addininsa yadda yaga dama .