Nigeria ta gano ma'aikata 20,000 na bogi

Hakkin mallakar hoto Reuters

Gwamnatin Najeriya ta ce ta gano cewa an sanya ma'aikata 20,000 na bogi a jerin ma'aikatun tarayya na kasar.

Ma'aikatar kudin kasar ta ce wani binciken da ta yi ya nuna cewa ana karya ana cire albashin ma'aikatan na bogi.

Ma'aikatar ta ce ta yi tsimin kusan Naira bilyan-biyu-da-dubu-dari-ukku a kudin albashin watan Fabrairu bayan ta tace yawan ma'aikatan.

Ta ce binciken na daga cikin kokarin da gwamnatin tarayya ke yi na yaki da cin hanci da rashawa da kuma inganta aikin gwamnati.