An gurfanar da Abba Moro a gaban kotu

Image caption Abba Moro na cikin ministocin Goodluck Jonathan da ake tuhuma da aikata laifuka.

An gurfanar da tsohon ministan harkokin cikin gida na Najeriya, Abba Moro, a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, bisa zargin sa da hannu a cuwa-cuwar daukar ma'aikata a shekarar 2014.

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattali arzikin Najeriya ta'annati, EFCC tana tuhumar Abba Moro da laifukan da ke da alaka da halasta kudin haram da cuwa-cuwa.

A cewar EFCC, Abba Moro ya karbi kudi daga wajen masu son a dauke su aiki a hukumar shige-da-fice ta kasar, ta hanyar sayar musu da takardun neman aiki.

Ta kara da cewa ma'aikatarsa ta samu N676, 675,000 daga sayar da takardun neman aiki a shekarar 2014, lamarin da ya saba wa dokar daukar aiki.

Tsohon ministan dai ya sha musanta wadannan zarge-zarge.