DiCaprio ya ci gasar Oscars

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sau shida Dicaprio ya so lashe gasar amma hakan bai yiwuw ba.

Fitaccen dan wasan kwaikwayon nan, Leonardo DiCaprio, ya lashe gasar Oscar a karon farko bayan da ya sha kashi sau shida.

DiCaprio ya lashe gasar ne saboda rawar da ya taka a fim din The Revenant.

An bayyana shi a matsayin jarumin jarumai a wajen bikin bayar da kyautar Academy karo na 88.

Kazalika, an bayyana Brie Larson, a matsayin 'yar wasan kwaikwayon da ta fi kowace mace a wannan shekarar sakamakon rawar da ta taka a fim din Room.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Brie Larson ta taka rawa a fim din Room.

Spotlight ya samu kyautar wanda ya fi iya daukar hoto na bana saboda rawar da ya taka a fim din Mad Max: Fury Road, wanda ya samu kyautuka shida rigis.

Mark Rylance ne ya lashe kyautar dan wasan da ya fi shahara cikin wadanda suka taimaka wa babban jarumi, yayin da Briton Sam Smith ya ci kyautar wanda ya fi iya waka a bana.