Iraki: Dan kunar bakin wake ya hallaka mutane

Hakkin mallakar hoto REUTERS
Image caption Iraki na fama da matsalar hare-hare

Jamia'i a Iraki sun ce a kalla mutane 20 ne suka mutu a wani harin kunar bakin wake da aka kai garin Muqdadiya da ke gabashin kasar.

Wasu fiye da 40 kuma sun jikkata.

Dan kunar bakin waken ya sanya bam din ne a cikin rigarsa yayin da ake jana'izar wani mayakin sa kai dan shi'a.

Zuwa yanzu dai babu wanda ya dauki alhakin kai harin amma ana zargin mayakan kungiyar IS ne.

A ranar Lahadi ma mayakan na IS sun kai wani hari makamancin wannan a wani yankin da mabiya shi'a suka fi yawa a wajen birnin Bagadaza, inda gomman mutane suka mutu.

Karin bayani