Mun mika Ese ga 'yan sanda - Sarkin Kano

Hakkin mallakar hoto Getty

Mai martaba sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II ya yi karin haske kan batun wata yarinya da ake zargin cewa wani dan Kano ya dauko ta daga jihar Bayelsa, ya musuluntar da ita ya kuma je da ita Kano sarki ya daura masu aure, an kuma hanata komawa wajen iyayen ta.

Sarkin na Kano, ya ce babu gaskiya a batun cewa an daura musu aure, kuma tuni ya bayar da umarnin a mikata ga 'yan sanda don mayar da ita garinsu.

Batun yarinyar dai mai suna Ese Rita na daga cikin wadanda suke daukar hankula a kafofin sada zumunta na Najeriya.

Ga dai karin bayanin da Sarkin ya yi wa wakilinmu Yusuf Ibrahim Yakasai:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti