Majalisar wakilan Nigeria za ta sayi motoci

Hakkin mallakar hoto national assembly
Image caption 'Yan majalaisar sun ce suna bukatar motoci domin gudanar da ayyukansu.

Majalisar wakilan Najeriya ta ce tana nan kan bakanta na shirin sayen motoci ga mambobinta domin yin aikin sa ido kan ma'aikatun gwamnati.

Wasu rahotanni da aka wallafa a wasu jaridun kasar dai sun nuna majalisar ta dakatar da shirin sayen motocin.

Sai dai a hirar sa da BBC, Hon Abdurrazak Namdas, shugaban kwamitin watsa labarai na majalisar wakilan, ya ce suna nan suna shirin sayen motocin.

Namdas ya kara da cewa za su sayi motocin ne saboda gudanar da ayyukan da suka rataya a kan su, da kuma zarar an gama batun kasafin kudin bana ne ake sa ran sayo su.

Wasu 'yan Najeriya dai na korafin bai kamata a sayo motocin ba, saboda matsalar da tattalin arzikin kasar ke fuskanta, da kuma halin kunci na rashin abin hannu da talakawa ke ciki.

Maimakon sayan motocin, kamata ya yi a zuba kudin dan ayyukan ababen more rayuwa da talakawa za su amfana da su.

Ga yadda hirar tasa ta kasance da Halima Umar Saleh:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti