Za a fadada kai kayan agaji Syria

Yara sun samu walwala bayan dakatar da bude wuta a Syria
Image caption Yakin basasar Syria ya daidaita yawancin sassan kasar.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce tana shirin fadada ayyukanta na kai kayan agaji ga al'umomin da aka yi wa kawanya a rikicin Syria daga ranar Litinin.

Ta shaida wa BBC cewa tare da abokan hadin-gwiwarta sun yi niyyar kai abinci da ruwan sha da kuma magunguna wa sama da mutum dubu dari da hamsin.

Sanarwar Majalisar Dinkin Duniyar na zuwa ne a rana ta biyu ta yarjejeniyar dakatar da bude-wuta a yakin da ake yi a Syria, duk kuwa da cewa bangaren gwamnati da na 'yan tawaye na zargin juna da saba wa yarjejeniyar.

Sai dai wani bangaren 'yan tawayen da babu gara ba dadi, bayan haka ma yanayin da ake ciki ya fi yanayin da aka fada gabannin cimma yarjejeniyar dakatar da bude-wutar nesa ba kusa ba.

Mutane sama da dubu dari biyu da hamsin ne suka rasa rayukansu tun fara yakin basasar Syria kusan shekaru biyar, ya yin da wasu miliyan goma sha uku suka rasa muhallan su.