'Yan sandan Nigeria sun kai Ese Rita Abuja

Image caption Sarki Sanusi II ya nuna damuwa kan yadda rundunar ta gaza mika yarinyar ga jihar ta Bayelsa.

A Najeriya, kakakin rundunar 'yan sandan kasar shiyya ta daya da ke Kano, Rilwanu Ringim, ya tabbatar wa da BBC cewa 'yan sanda sun tafi da yarinyar nan 'yar jihar Bayelsa, Ese Rita da kuma mutumin da aka yi zargin ya dauko ta zuwa Abuja.

Ana dai zargin mutumin, mai suna Inusa, ya kai ta Kano ne inda ya Musuluntar.

Batun dai ya je gaban Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II a watan Agustan da ya gabata, kuma Sarkin ya mika shi ga hukumar Shari'a domin ta gudanar da bincike.

Sanarwar da fadar Sarkin ta fitar ta bayyana cewa, "Sakamakon binciken ya nuna cewa yarinyar ba ta kai shekarun da za ta iya yin hukunci a game da rayuwarta ba tare da bin umarnin iyayenta ba.Don haka ne muka bukaci Babban jam'in 'yan sanda shiyyar Kano ya mika ta ga takwaransa na shiyyar jihar Bayelsa domin ya kai ta wajen iyayenta".

Sarkin na Kano ya kara da cewa tun daga lokacin bai sake yin tunani kan yarinyar ba domin ya yi zaton an riga an mika ta ga iyayenta.

A cewarsa, ya kamata babban jami'in 'yan sanda shiyya Kano ya yi bayanin dalilin da ya sa bai mika ta ga takwaransa da ke Bayelsa ba.

Sarkin ya kuma yi kira ga 'yan Najeriya da su guji watsa labarai na karya, yana mai cewa hakan zai kawo rashin jituwa tsakanin al'umomin kasar.

Batun dai ya janyo cece-kuce musamman a shafukan sada zumunta na zamani.