Ta yiwu a fadada takunkumin Korea ta Arewa

Shugaba Kim na Korea ta Arewa Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Gwajin makamin nukiliyar arewa na shan cece-kuce a kassahen duniya.

Wasu Jakadun Majalisar Dinkin Duniya sun ce idan an jima ne kwamitin sulhun majalisar zai kada kuri'a a kan batun fadada takunkumin da aka kakaba wa kasar Korea ta Arewa.

Matakin dai ya biyo bayan gwajin makamin nukiliyar da Korea ta arewar ta yi a watan Janairun da ya wuce.

Takunkumin dai zai shafi duba duk wani kayan da zai shiga kasar, ko kuma za a fitar da shi ta sama, da kuma haramta yin kowane irin cinikin makamai da kasar, matakin da zai magance raunin da ke tattare da takunkumin da aka kakaba mata tun da farko.

A watan Junairun wannan shekarar ne Korea ta Arewa ta yi gwajin makamin kare dangi mai cin dogon zango, da aka hada da sinadrin Hydrogen, lamarin da ya harzuka kasashen duniya tare da yin Aallawadai da hakan.

Sai dai Korea ta Arewar ta nanata cewa gwajin na tauraron dan adam ne, kuma gwaje-gwajen makaman nukiliya da ta sha yi a baya ba masu cutarwa ba ne.